Connect with us

News

Dakarun Amotekun Sun Kame Ƴan Arewa 38 A Ondo

Published

on

images (3)

Ƙungiyar Amotekun mai samar da Tsaro a yankin jihohin yammacin Najeriya ta sanar da kama mutane 38 da aka samu a cikin wata mota kirar Mercedes-Benz sabuwa, waɗanda ake zargin sun fito ne daga arewacin ƙasar.

Bayanai sun ce an kama mutanen ne a cikin sabuwar motar daukar kaya mai lambar rajista ta Jihar Jigawa.

Advertisement

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Da Wasu Mutane 5 A Kano

A yayin bincike, an gano cewa waɗanda ake zargin ba su iya bayyana takamaiman inda zasu je a jihar ta Ondo ba.

Da yake magana kan lamarin, Kwamandan Amotekun na Jihar Ondo, Akogun Adetunji Adeleye, wanda ya tabbatar da kamen a ranar Litinin, ya ce mutanen ba su da wata tabbatacciyar manufa ko inda wannan balaguro nasu ya nufa.

Advertisement

Ya ƙara da cewa wurin da direban ya ce ya ɗauko su na daga cikin wuraren da ake ganin akwai matsalolin tsrao da kuma masu tsatsauran ra’ayi.

Kwamandan ya ce, nan ba da jimawa ba za’a fara bincike, tare da gurfanar da duk wanda ake zargi a gaban kotu.

Advertisement

Shugaban Amotekun ya kuma roƙi mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, yana mai tabbatar da cewa lamarin yana ƙarƙashin kulawa.

Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaron jihar.

Advertisement

Wata majiya ta ce an samu ɗaya daga cikin mutanen da ake zargin da wani kayan sarki da aka rubuta kalmar “Commander” a jikinta, tare da wasu kayan tsafe-tsafe.

To amma ya shaida wa masu bincike cewa shi mafarauci ne, kuma wannan kaya na aikinsa ne, sai dai bai iya bayyana takamaiman inda zashi a jihar ba.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending