News
Yawaitar Amfani Da Dakarun Soji A Ayyukan Tsaron Cikin Gida Na Raunata Rundunar ‘Yan Sanda — Buratai
Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya yi gargaɗin cewa yawaitar amfani da rundunar soji wajen ayyukan tsaron cikin gida a Najeriya na raunana ƙarfin rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Buratai ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabin buɗe taro a bikin tunawa da mazan jeya na Rundunar Sojin Najeriya na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce duk da cewa shigar sojoji cikin harkokin tsaro na cikin gida na kawo kwanciyar hankali a cikin gaggawa, hakan na haifar da dogaro mai ƙarfi da ke hana bunƙasar hukumomin da kundin tsarin mulki ya dorawa alhakin tsaron cikin gida.
A halin yanzu, ana iya ganin sojoji a kusan dukkanin jihohin ƙasar 36, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda suke gudanar da ayyukan tsaro na yau da kullum.
Sai dai Buratai ya ce wannan yanayi na barazana ga cigaban rundunar ‘yan sanda da hukumomin leƙen asiri, tare da rage musu ‘yancin cin gashin kansu.
“Yawaitar tura sojoji cikin harkokin tsaron cikin gida na kawo kwanciyar hankali nan take, amma yana haifar da wani zagaye na dogaro da ke raunata ƙarfin ‘yan sanda ,” in ji Buratai.
Ya ƙara da cewa hakan ya janyo wani hatsarin rashin daidaito, inda sojoji ke ɗaukar nauyin da ya wuce ƙarfin da aka tanada musu, ana karkatar da kasafin tsaro zuwa ayyukan ‘yan sanda na yau da kullum,
Sai dai ya jaddada cewa tsaron cikin gida ya kamata ya kasance karkashin jagorancin farar hula, musamman rundunar ‘yan sanda da hukumomin leƙen asiri na jihohi.
Akwai ayyukan tsaron cikin gida masu yawa da yakamata ace jami’an ‘yan sanda ne ke yi a Najeriya
A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ya zama dole a haɗa kai domin dakile yadda ƙungiyoyin aikata laifi ke amfani da hanyoyin sufuri na cikin gida wajen jigilar makamai, miyagun ƙwayoyi da sauran haramtattun kaya.
Ya ce ba za a iya magance matsalar tsaro ta hanyar amfani da rundunar soji kaɗai ba, sai an haɗa da hukumomi Tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da al’umma baki ɗaya.
“Tsaro alhaki ne na kowa da kowa, ba na sojoji kaɗai ba,” in ji Musa.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar barazanar ‘yan fashi da makami, ‘yan ta’adda da cibiyoyin aikata laifi, waɗanda ke amfani da hanyoyin sufuri na cikin gida wajen safarar makamai da kayayyakin haram.
