Connect with us

News

Hasashen Sauya Shekar Gwamna Kano Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa APC Bai Tabbata Ba Har Yanzu

Published

on

Gwamnan Kano Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Daya Wajen Tafiye tafiye Zuwa Kasashen Waje Cikin Watanni 9.

Duk da rade-radin da ke yawo a fagen siyasar Kano cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a  Litinin, 12 ga Janairu, 2026, har zuwa wannan lokaci babu wata alama ko sanarwa a hukumance da ke tabbatar da faruwar hakan.

A yan kwanakin nan ne aka yi ta jin jita-jitar cewa gwamnan zai fice daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin yan siyasa, magoya baya da kuma jama’ar jihar.

Advertisement

‎Yawaitar Amfani Da Dakarun Soji A Ayyukan Tsaron Cikin Gida Na Raunata Rundunar ‘Yan Sanda ‎ ‎ ‎ ‎ ‎ — Buratai

Amma har zuwa yanzu babu wata sanarwa daga gwamnati ko daga bangaren gwamnan da ke nuni da cewa an dauki matakin sauya shekar.

Sai dai a safiyar Ranar Litinin an ga karuwar jami’an tsaro a kofar gidan gwamnatin Kano, lamarin da ya kara rura wutar jita-jitar siyasar.

Advertisement

Jami’an tsaron sun tsaurara matakan bincike ga masu shiga da fita, abin da ya janyo hankalin jama’a da masu wucewa.

Wasu yan siyasa da mazauna birnin Kano sun bayyana cewa tsauraran matakan tsaro na iya kasancewa da nasaba da muhimman taruka ko kuma matakan kariya na yau da kullum, waɗanda ba lallai ne ya danganci sauya shekar gwamnan ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIER RADIYO

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending