Connect with us

News

Yan Kasuwa Ku Ji Tsoron Allah Ku Guji Tayar Da Farashin Kayayyakin Masarufi A Lokacin Azumi — Sarkin Kazaure

Published

on

MARKET1 (1)

Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr. Najib Hussaini Adamu, ya bukaci ’yan kasuwa a Jihar Jigawa da su ji tsoron Allah tare da gujewa tayar da farashin kayayyakin masarufi, musamman a lokacin watan azumin Ramadan.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin wani taro na musamman domin maraba da watan Ramadan, inda aka kaddamar da wata mukala mai taken “Sababbin Hanyoyin Kasuwanci na Zamani: Amfani da Illolinsu”, wanda Cibiyar Marigayi Ado Namagaji da ke Kazaure ta shirya.

Advertisement

Yan Kasuwa Ku Ji Tsoron Allah Ku Guji Tayar Da Farashin Kayayyakin Masarufi A Lokacin Azumi — Sarkin Kazaure

Taron, wanda aka gudanar a dakin taro na Ibrahim Dantunku da ke Kazaure, ya hada da yaye dalibai 80 da suka kammala karatun littafin Fiqhul Muyassar.

Advertisement

Sarkin Kazaure ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu ’yan kasuwa ke kara tsawwalawa al’umma ta hanyar tayar da farashi a lokacin da ake bukatar sassauci da tausayi, musamman a watan Ramadan. Ya tunatar da su irin hukuncin da Musulunci ya tanadar wa masu cutar da al’umma ta hanyar cin hanci da zalunci a ranar Lahira.

Ya kuma jinjinawa Cibiyar Marigayi Ado Namagaji bisa shirya taron maraba da Ramadan, tare da yin addu’ar Allah Ya karɓi ibadun Musulmi a watan mai alfarma. Haka kuma Sarkin ya yabawa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa ayyukan raya kasa da take gudanarwa a fadin jihar.

Advertisement

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Kazaure, Mansur Usman Dabuwa, ya jaddada kudurin majalisar karamar hukumar na ci gaba da ba wa ilimi fifiko, domin samar da al’umma nagari. Ya kuma yaba wa cibiyar Ado Namagaji bisa rawar da take takawa wajen bayar da ilimi da tarbiyya, yana mai cewa karamar hukumar za ta ci gaba da ba ta goyon baya.

Shi ma Babban Bako mai Jawabi, Dr. Musa Adamu, ya bayyana cibiyar a matsayin wacce ta yi fice wajen ilimi da tarbiyya, inda ya yi alkawarin bayar da tallafin naira miliyan daya domin karfafa gwiwar malamai.

Advertisement

Haka zalika, wakilin Gwamnan Jihar Jigawa ya bayar da tallafin naira miliyan biyu domin bunkasa harkokin koyo da koyarwa a makarantar.

A yayin taron, an gabatar da mukaloli daban-daban daga malaman addinin Musulunci. Daga ciki akwai Malam Jamilu Usman, wanda ya gabatar da mukala kan sabbin hanyoyin kasuwanci a mahangar Musulunci, da kuma Malam Ali Aliyu Daura, wanda ya gabatar da mukala mai taken “Biyar kafin Biyar.”

Advertisement

A karshen taron, Sarkin Kazaure ya rarraba takardun shaidar kammala karatu ga daliban Fiqhul Muyassar, tare da sanya musu albarka.

Taron ya samu halartar manyan baki da dama, ciki har da Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, kuma Dan Majalisar da ke wakiltar Karamar Hukumar Roni, Dr. Mas’ud Adamu, da Magajin Malam, da sauran manyan baki daga ciki da wajen Karamar Hukumar Kazaure.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending