News
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, Ya Kori kwamishina
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya sallami Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima, daga muƙaminsa.
Sallamar ta fara aiki nan take, kamar yadda wata sanarwa da Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Litinin ta bayyana.
Sanarwar ta ce matakin na daga cikin shirin gwamnatin jihar na sake fasalin majalisar zartarwa, domin ƙara inganta ayyukan gwamnati da kuma ƙarfafa tsarin shugabanci a jihar.
Gwamna Bala Mohammed ya gode wa Galadima bisa gudummawar da ya bayar yayin da yake riƙe da muƙamin, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta tabbatar wa al’ummar Bauchi cewa za ta ci gaba da ba da muhimmanci ga zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a sanar da wanda zai maye gurbinsa nan gaba..
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
