News
Shugaba Tinubu Ya Umarci Masu Son Takara A 2027 Su Ajiye Mukamansu Kafin Karshen Maris
Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙarƙashin gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓukan shekarar 2027 da su ajiye mukamansu kafin ranar 31 ga watan Maris.
A sanarwar da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), Dewan Goshit, ya fitar, ya bayyana cewa wannan umarni ya shafi dukkan jami’an gwamnati masu son shiga takarar zaɓe.
Gamayyar Ƙungiyoyin APC sun amince da kungiyar Sen Yari The Renewed Hope Network TRN
Sanarwar ta ƙara da cewa matakin na da nufin tabbatar da gaskiya da daidaito, tare da ba wa masu neman takara damar fafatawa cikin yanayi mai adalci kafin a fara shirye-shiryen zaɓen.
The CABLE
Advertisements
