Connect with us

News

Yan Ta’adda Sun Buƙaci Naira Biliyan 3.52 Domin Sakin Mutane 176 da Aka Sace A Kwara

Published

on

yan bindiga sun sace mutane
Advertisements
ads

Rahotanni daga Jihar Kwara na cewa wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun buƙaci a biya su kuɗin fansa har naira biliyan 3.52 domin sakin mutane 176 da aka sace a ƙaramar hukumar Kaiama.

‎Majiyoyi sun ce waɗanda aka sace, mafi yawansu mata da ƙananan yara, an yi awon gaba da su ne a watan Fabrairun 2026 lokacin da aka kai hare-hare a ƙauyen Woro da wasu yankuna da ke makwabtaka da shi.

Shugaba Tinubu Ya Umarci Masu Son Takara A 2027 Su Ajiye Mukamansu Kafin Karshen Maris

‎A cewar rahotannin, maharan sun ƙayyade naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum, kuma sun riga sun tuntubi wasu masu shiga tsakani domin fara tattaunawa da iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma jami’an gwamnati.

‎Sai dai tattaunawar na fuskantar tangarda, yayin da gwamnatin Jihar Kwara ke nuna rashin amincewa da biyan kuɗin fansa.

‎A wani faifan bidiyo da ake zargin maharan ne suka fitar, an ga wasu daga cikin waɗanda aka sace, ciki har da mata masu goyon jarirai da yara, cikin mawuyacin hali. Maharan sun kuma yi zargin cewa hukumomi na rage girman lamarin.

Advertisement

‎A nata bangaren, gwamnatin jihar ta ce tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tantance sahihancin bidiyon da kuma ƙara ƙaimi wajen ganin an ceto mutanen cikin koshin lafiya, duk da cewa har yanzu ba a samu wani ci gaba mai ma’ana ba.

 

 

SHAHARA REPORTS 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending