News
Tankar Dakon Man Fetur Ta Fadi Ɗauke Da Kimanin Lita 50,000 A Kaduna
Wata tankar dakon man fetur ta faɗi a ranar Lahadi a NEPA Roundabout da ke birnin Kaduna.
Hakan na cikin wata sanarwar da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna ta fitar a ranar Lahadi 8 ga Fabrairu 2026.
Direba Da Mataimakinsa Sun Rasa Rayukansu A Fashewar Tanker Man Fetur
Sanarwar ta bayyana cewa tankar da ta faɗi na ɗauke da kimanin lita 50,000 na man fetur.
A cewar sanarwar, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna ta haɗa kai da sauran hukumomin tsaro da na ceto domin killace yankin, daidaita zirga-zirga, tare da sa ido kan fitar da man fetur domin hana tashin gobara ko wata matsala.
Sanarwar ta ƙara da cewa an shawo kan lamarin cikin lokaci, tare da kira ga direbobin manyan motoci da su rika bin ƙa’idojin tsaro domin guje wa aukuwar irin wannan hatsari a gaba.
