News
Na gayawa Buhari idan sojojin shi suka gaza, to mu gwamnoni zamu dauko hayar sojojin da zasu kashe ‘yan Bindiga daga kasar waje -El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, idan sojojin Najeriya suka gaza, to su zasu dauko hayar sojoji daga kasar waje da zasu kashe ‘yan Bindiga.
Gwamnan ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi da ‘yan Jarida, ya koka da cewa matsalar tsaron ta yi yawa.
Yace tabbas ba zasu zura ido suna gani ana kashe mutane da sace su ba.
Yace hakan yunkuri ne na lalata tattalin arzikin Kaduna, da Arewacin Najeriya dama kasar baki daya.
Yace an ga mutane na zuba jari a Kaduna shine kawai aka bullo da wannan abu dan kassara jihar.
Yace amma shugaba Buhari ya bashi tabbacin magance matsalar.
Hakazalika
Kwantar da hankali: Nan da ‘yan watanni zamu gama da ‘yan Bindiga
-Shugaba Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa, nan da ‘yan watanni za’a gama da ‘yan Bindiga.
Shugaban ya bayyanawa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai hakane a ganawar da suka yi a fadarsa.
Hakan na zuwane bayan harin da ‘yan Bindigar suka kai kan jirgin kasan dake jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
Saidai Gwamna El-Rufai yace idan sojojin Najeriyar suka gaza, to su zasu dauko hayar sojojin da zasu kashe ‘yan Bindigar.
