News
Lauyoyin Gwamnatin Kano Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki A Fadin Jihar
Lauyoyin da ke aiki a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano sun sanar da cewa za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga tsakar daren ranar 11 ga watan Maris, 2026, sakamakon abin da suka bayyana a matsayin tauye musu haƙƙoƙinsu da kuma gazawar gwamnatin jihar wajen aiwatar da alkawuran da ta ɗauka.
Shugaban ƙungiyar Law Officers Association of Nigeria (LOAN), reshen Jihar Kano, Barista Aminu Abdullahi Shams, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Talata.
Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka
A cewarsa, matakin shiga yajin aikin ya biyo bayan gaza samun mafita duk da tattaunawa da dama da ƙungiyar ta yi da jami’an gwamnati a lokuta daban-daban.
Barista Shams ya ce ƙungiyar ta aike da wasiƙa ga Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano mai taken “Sanarwar Fara Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani”, inda ta bayyana dalilan da suka sa suka yanke wannan hukunci.
Ya ce tun a shekarar 2025 suka fara gabatar da koke-kokensu ga gwamnati, ciki har da wasiƙar da suka aike a ranar 18 ga watan Yuni, 2025, da kuma rahoton wani kwamiti na musamman da gwamnatin jihar ta kafa domin duba matsalolin.
Sai dai ya ce duk da cewa an amince da wasu daga cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar, har yanzu ba a aiwatar da su ba.
Haka kuma ya ce wani taron sasanci da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da kuma Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a suka kira bayan wata sanarwar da ƙungiyar ta bayar a watan Janairu 2026, bai samar da wani sakamako ba.
A cewar shugaban ƙungiyar, a baya sun dakatar da wani yajin aiki da suka shirya yi a watan Fabrairu 2026 bayan roƙon gwamnati, inda suka ba ta wa’adin kwanaki 28 domin ta magance matsalolin, amma har yanzu babu wani ci gaba.
Ya ce bayan wani taron ƙungiyar da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris, 2026, mambobinta suka yanke shawarar fara yajin aikin bisa tanadin sashe na 41 da na 42 na dokar Trade Disputes Act ta 1976.
Ƙungiyar ta ce wasu daga cikin matsalolin da suka haifar da yajin aikin sun haɗa da rashin biyan wasu alawus-alawus tun daga shekarar 2017, rashin biyan sabbin lauyoyin gwamnati albashin watanni biyu, da kuma rashin aiwatar da karin matsayi ga wasu lauyoyi tun shekarar 2022.
Sauran matsalolin sun haɗa da rashin motocin aiki ga lauyoyin gwamnati, ƙarancin ofisoshi da bandakuna a wuraren aiki, da kuma rashin biyan wasu alawus da ake bai wa takwarorinsu a wasu jihohi.
Ƙungiyar ta gargaɗi cewa idan har gwamnati ba ta magance matsalolin ba, dukkan lauyoyin gwamnati a jihar za su janye ayyukansu gaba ɗaya.
Masu sa ido kan harkokin shari’a na ganin cewa yajin aikin na iya janyo tsaiko ga gudanar da shari’o’i da kuma wakilcin gwamnatin jihar a kotuna a faɗin Jihar Kano.
