Connect with us

News

Karo Da Tsuntsaye Ya Tilastawa Jiragen Sama Biyu Saukar Gaggawa A Abuja

Published

on

1776384089487

A Najeriya, wasu jiragen sama guda biyu sun fuskanci matsalar karo da tsuntsaye a ranakun Talata da Laraba, lamarin da ya tilasta musu saukar gaggawa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kamfanin sufurin jiragen sama na United Nigeria Airlines ya tabbatar da cewa daya daga cikin jiragensa mai lamba UN0579 ya gamu da wannan matsala ne a ranar Talata, bayan ya taso daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Kano zuwa Abuja.

Advertisement

‎Wani Mutum Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Biyo Bayan Daɓa Masa Wuƙa Saboda Naira 200 ‎

A cikin wata sanarwa, kamfanin ya ce jirgin kirar CRJ-900 ya hadu da tsuntsu ne yayin saukarsa, lamarin da ya sa aka janye shi daga aiki nan take domin gudanar da cikakken binciken fasaha da kuma gyare-gyare kafin a sake mayar da shi aiki.

Advertisement

Haka kuma, kamfanin ya bayyana cewa wannan shi ne karo na biyar da jiragensa ke fuskantar irin wannan matsala tun daga watan Janairun shekarar 2026, amma ya ce ana tafiyar da dukkan lamarin bisa ka’idojin tsaro na harkokin sufurin jiragen sama.

A wani bangare, an samu makamancin wannan lamari a ranar Laraba, inda wani jirgi da ya taso daga Fatakwal shi ma ya fuskanci karo da tsuntsaye kafin saukarsa a Abuja, wanda ya tilasta masa sauka cikin gaggawa.

Advertisement

Masana harkokin jiragen sama na cewa irin wannan hadari na faruwa ne galibi a lokacin tashi ko saukar jirage, lokacin da tsuntsaye ke shawagi a kusa da filayen jiragen sama.

 

Advertisement

BUSINESS DAY

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending