Connect with us

Opinion

Gwamnatin Tarayya Ta Ci Gaba Da Aikin Titin Kano-Gwarzo-Dayi Sakamakon Biyan Diyya Da Gwamnatin Abba Ta Yi

Published

on

IMG 20260502 165155 278

DAGA ABBA ANWAR 

Idan har babban titin Kaduna na Eastern Bypass, da a ka fara tun shekarar 2002, da babban titin Abuja-Lokoja, da a ka fara 2006, da titin Kano-Maiduguri, da a ka fara 2007, da titin Sokoto – Tambuwal – Jega-Kontagora, da a ka fara 2009, da titin Abuja-Minna, da a ka fara 2010, ba a bude baki kullum a na ihun cewa an yi watsi da su ba, to lallai kuwa bai kamata ai ta bude baki a na ihun wai titin Kano-Gwarzo-Dayi, wanda ya na daya daga cikin ayyukan da mataimakin shugaban majalisar dattawa ta Kasa, Sanata Barau Jibrin ya sa a matsayin cikin manyan ayyukansa, da a ka fara a Watan Juli na shekarar 2021, a na cewa wai ya yi watsi da aikin ba. Ina ga akwai son zuciya a harkar.

Advertisement

Shi fa titin Kano-Gwarzo-Dayi wanda na daga cikin manyan ayyukan Sanata Barau, an taba samun tsaiko, sakamakon rashin biyan diyya ga mutane da gwamnatin baya ta yi. Amma kuma aiki ya dawo ganga-ganga a cikin watan Fabrairu na dai shekarar da muke ciki, ta 2026, sakamakon biyan diyya ga dubban mutane da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi.

Duk da haka, a kan dai wannan titin na hanyar Gwarzo din, Sanata Barau ya yi rawar gani wajen ya kara sa tsabar kudi dan cigaban aikin, a kasafin kudi na 2026, har Naira Bilyan Talatin da Bakwai (N37,000,000,000).

Advertisement

Duk fa da cewar Sanatan ya yi wannan kokarin kuma ga shi har an dawo a na ci gaba da aikin titin, duk da haka fa a halin da a ke ciki akwai manyan titunan da har yanzu an bar su a shantake a fadin sassan kasar nan. Bisa dalilai kala – kala.

Akwai irin titin Makurdi-Naka-Adoka-Ankpa da a ka fara tun 2012, da titin Calabar-Itu-Ikot Ekpene, da a ka fara 2010, ga titin Benin-Sapele-Warri da a ka fara 2009, ga titin Enugu – Onitsha da a ka fara 2013, sai aikin raba titin Kano-Katsina da a ka fara 2013, wanda dan kwangilar ya bar aikin tun 2022, tare da tulin wasu manyan ayyukan.

Advertisement

Sai kuma titin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano shi ma wani abin kallo ne da kuma misali. Kodayake an dan dawo kan sa yanzu.

Saboda haka ni a gani ba, sukar Sanata a kan wannan babban aikin na Kano-Gwarzo-Dayi, ba wai kawai bai kamata ba, a’a ba daidai ba ne. Idan da gyara a gyara min. Ga shi dai kokarin da ya yi, na sake sa wasu makudan kudade kan aikin. Tare da cewa kuma, har ma an dawo an ci gaba da aikin tun watan Fabrairu na wannan shekarar da muke ciki.

Advertisement

Daga cikin ire-iren abubuwan da a ke ta zargin Sanata da cewar wai ya yi watsi da su, har da maganar Cibiyoyin horaswa na hanyoyin zamani wato “E-learning Centres” da za a yi a kananan hukumomi guda biyar. Wanda wannan shiri ne tare da hadin gwuiwa da hukumar NITDA.

A kananan hukumomin Tofa da Gwarzo da Kabo da Bichi kuma Dambatta. A ka ce za a yi wadannan cibiyoyi.

Advertisement

Abinda ya faru shine, ba fa wai an yi watsi da cibiyoyin ba ne haka siddan. A’a. Sanatan dai a baya ya yi kokarin samar da rassa na babbar Jami’ar nan ta kasa, wato “National Open University of Nigeria (NOUN)” a dukkanin kananan hukumomi 13 da suke karkashin mazabarsa ta Sanatan Kano ta Arewa. Saboda haka wadancan cibiyoyin horaswa din na kananan hukumomi 5 din sai a ka mayar da su rassan jami’ar NOUN.

Wannan kuma ai gagarumin cigaba a ka samu. Maimakon da cibiyar horaswa, yanzu waje ya zama reshen jami’a. Ai likkafa ta yi gaba za a ce.

Advertisement

Wani abin da kuma a ke ta zargin Sanata Barau da cewar wai ya yi watsi da shi shine, maganar tallafin noma din nan da za a ba matasa da su ka gama karatun Digiri a jami’a. Tallafin daga Naira Milyan Biyu zuwa Milyan Uku zuwa Milyan Biyar din nan, kan noman shinkafa da masara.

Wanda a karkashin shirin a ka ce za a tallafawa matasan da suka fito daga shiyyar Arewa Maso Yamma, su dari biyar da hamsin da takwas (558). Shi wannan shirin an yi shine karkashin wani shiri na musamman na Sanata Barau na harkar noma, mai suna “Barau Initiative for Agricultural Revolution in the North West (BIARN).” Tare da Bankin Manoma, wato Bank of Agriculture (BOA).

Advertisement

To Alhamdulillah, sai ga shi a wata sanarwa da yau ba ta fi kwana 4 ba, da Mai Bayar da Shawara na Musamman kan Yada Labarai, na Sanata din, Ismail Mudassir ya fitar da sanarwar cewa, duk wadanda a ka zaba saboda su zama masu amfana daga shirin na musamman, bayan da a ka tantance su, su cigaba da hakuri da jiran fara shirin ba da wata dadewa ba.

A sanarwar ya ce, daga bangaren Sanata an gama komai. Kawai abinda ya rage shine da zarar Bankin Manoma din ya samu an sakar masa kudi daga gwamnatin tarayya, komai zai fara wakana. Saboda haka ba kamar yadda wasu ke ta zancen cewa wai an yi watsi da abin ba ne.

Advertisement

Gaskiya ne suka da yin kalubale a siyasa halas ne, amman masu ma’ana sun fi kyau. Allah Ya iya mana

Anwar ya rubuto wannan daga Kano

Advertisement

Asabar, 2 ga watan Mayu, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending