News
Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Kisa Ta Rataya A Kano
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum mai suna Abdulaziz Umar, bayan samun sa da laifin kashe Mubarak Salisu.
KotunKotun ta kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai kan laifin fashi da makami.
Yadda Siyasa Ke Mayar da Matasan Kano ‘Yan Daba
Mai shari’a Zuwaira Yusuf, wadda ta jagoranci shari’ar, ta ce bangaren masu gabatar da kara sun gabatar da gamsassun hujjoji da suka tabbatar da laifukan da ake tuhuma ba tare da wata tantama ba.
“Na yanke maka hukuncin daurin rai da rai kan laifin fashi da makami, sannan kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan kai har sai an tabbatar da mutuwarka,” in ji ta.
Tun da farko, lauyar gwamnati, Aisha Salisu, ta bayyana wa kotu cewa lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Oktoba, 2020 a filin Race Course da ke Badawa Layout a Kano, lokacin bikin ranar samun ‘yancin kai.
Ta ce wanda ake tuhuma ya caka wa mamacin wuka a ciki da hannu, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa, sannan ya kwace wayar salula kirar Samsung mallakin mamacin.
A yayin shari’ar, bangaren masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu guda biyar tare da hujjoji domin tabbatar da zargin.
Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin.
Lauyan wanda ake kara, Ya’u Abdullahi, ya gabatar da shi a gaban kotu domin kare kansa.
Masu gabatar da kara sun ce laifukan sun sabawa sashe na 298 da na 221 na kundin dokokin Penal Code.
