Connect with us

News

An Fizgo Shugaban Jam’iyyar NDC Daga Kan Babur Yayin Da Aka Kona Fastocin Obi Da Kwankwaso A Kano

Published

on

FB IMG 1780169655213 768x538

An samu tashin hankali a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano bayan wasu matasa sun kona fastocin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a yayin da ake gudanar da wasu harkokin yaɗa manufofin jam’iyyar a yankin, inda aka ce wasu fusatattun matasa suka lalata kayayyakin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar tare da ƙona fastocin jagororinta.

Advertisement

Gwamnan Jigawa Ya Dakatar Da Hadimansa  Guda 4 

Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka janyo shugaban jam’iyyar NDC na Ƙaramar Hukumar Ungogo, Bilyaminu Bachirawa, daga kan babur yayin da rikicin ke faruwa.

Advertisement

Majiyoyi sun bayyana cewa Bachirawa ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu matasa suka bi shi, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin magoya bayan jam’iyyar a yankin.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jam’iyyar NDC ta tabbatar da Peter Obi a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, tare da ayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin abokin takararsa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Advertisement

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan abin da ya faru ba. Haka kuma, shugabannin jam’iyyar NDC a matakin jiha da na ƙasa ba su yi martani kan lamarin ba.

Sai dai masu ruwa da tsaki na ci gaba da kira ga magoya bayan jam’iyyun siyasa da su guji tayar da zaune tsaye tare da rungumar zaman lafiya domin tabbatar da an gudanar da harkokin siyasa cikin kwanciyar hankali da mutunta ra’ayin juna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending