Connect with us

News

Rundunar ‘Yan Sandan Kano Tayi Barazanar Kama Masu Amfani Da Talalmin Taya Akan Tituna

Published

on

1780740207419

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi matasa masu yin roller skating, wato amfani da talalmin taya a manyan tituna, gadoji, tana mai cewa duk wanda aka samu yana jefa rayuwar jama’a cikin hadari zai fuskanci hukunci.

A cewar rundunar, an lura cewa wasu matasa na manne wa motocin da ke tafiya domin karawa kansu gudu, lamarin da ka iya haddasa mummunan hadari ko asarar rayuka.

ARTV Ta Musanta Zargin Sare Bishiyoyi, Yayin Da The Historica Nigeria Ta Tsaya Kan Rahotonta

‘Yan sandan sun bayyana cewa manyan tituna an gina su ne domin zirga-zirgar ababen hawa kawai, ba domin irin wadannan wasanni ba.

Rundunar ta kuma bukaci iyaye, malamai da shugabannin al’umma su gargadi matasa kan wannan dabi’a mai hatsari.

Tana mai cewa duk wanda aka samu yana hana zirga-zirga ko kuma yana jefa rayuwarsa da ta wasu cikin hadari zai iya fuskantar kamu da gurfanarwa a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending