Connect with us

News

DSS Ta Kama Wasu Na Kusa Da Tsohon Minista Timipre Sylva Bisa Zargin Yunkurin Kifar Da Gwamnati Da Ake Masa ‎

Published

on

Timipre Sylva (1)
Advertisements
ads

Jami’an DSS sun kama akalla mutum biyar da ke aiki tare da tsohon Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, bisa zargin ɓoye bayanan da za su taimaka wajen gano inda yake, yayin da ake zarginsa da hannu a yunkurin kifar da gwamnati.

‎Ana zargin Sylva da hannu a wani yunkurin kifar da gwamnatin farar hula, zargi da har yanzu yake gaban kotu.

Rahotanni sun ce tsohon ministan ya ɓuya tun bayan da aka fara shari’ar, lamarin da ya sa ake ci gaba da gurfanar da shi ba tare da kasancewarsa a kotu ba.

DSS Ta Kama Wasu Na Kusa Da Tsohon Minista Timipre Sylva Bisa Zargin Yunkurin Kifar Da Gwamnati Da Ake Masa ‎

‎Bayanan da aka samu sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙara mai kunshe da tuhume-tuhume guda 13 kan wasu mutane bakwai da ake dangantawa da wannan zargi.

Laifukan da ake tuhumarsu da su sun haɗa da cin amanar ƙasa, haɗa baki domin kifar da gwamnati, shirya ayyukan ta’addanci da sauran laifukan da suka shafi barazana ga tsaron ƙasa.

Advertisement

‎Daga cikin waɗanda ake tuhuma akwai tsohon Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana, tsohon Kyaftin na Rundunar Ruwa Victor Erasmus Ochegobia, Sufeton ’Yan Sanda Ahmed Ibrahim, da Timipre Sylva, sai kuma Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Abdulkadir Sani. Haka kuma, wasu jami’an soja da ake zargi na fuskantar shari’a a kotun soja.

‎Wata majiya mai tushe daga hukumomin tsaro ta bayyana cewa mutanen biyar da aka gurfanar ma’aikata ne kuma amintattun na kusa da Sylva. A cewarta, ana zarginsu da kin bai wa masu bincike haɗin kai da kuma ɓoye bayanan da za su taimaka wajen cafke tsohon ministan.

‎Majiyar ta ce, saboda abin da ake zarginsu da aikatawa, su ma za su fuskanci shari’a domin kotu ta tantance gaskiyar zarge-zargen da ake musu.

‎Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Timipre Sylva ko lauyoyinsa da ke mayar da martani kan zarge-zargen da ake masa, yayin da shari’ar ke ci gaba a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

 

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending