News
Wani Likita Ya Rasu Mintuna 15 Bayan Isa Asibiti Domin Duba Marasa Lafiya A Kano
Wani babban likita a Jihar Kano ya rasu cikin rashin zato bayan ya fadi a sume mintuna 15 kacal da isarsa Arewa Surgery Hospital da ke unguwar Hotoro, inda ya amsa kiran gaggawa domin duba marasa lafiya da suka shafe sa’o’i suna jiransa.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, lokacin da likitan ya maye gurbin wani abokin aikinsa da ya kasa halartar aikin duba marasa lafiya kamar yadda aka tsara.
Wata Mota Ta Faɗa Cikin Kogin Mayo-Ine A Ngurore
Bayan isarsa harabar asibitin, an ce likitan ya fara jin jiri nan take bayan ya sauka daga motarsa, lamarin da ya sa ma’aikatan lafiya suka garzaya da shi zuwa sashen bayar da agajin gaggawa domin ceto rayuwarsa.
Sai dai duk da kokarin da likitoci suka yi na farfaɗo da shi, an tabbatar da rasuwarsa kimanin mintuna 15 bayan isarsa asibitin.
Bayanan faruwar lamarin sun fito ne daga Suleiman Harbo, wani mai taimaka wa Gwamnan Jihar Jigawa, wanda ya ce yana cikin ‘yan uwan marasa lafiyan da suka halarci asibitin a lokacin.
A cewarsa, ya kai mahaifiyarsa asibitin da misalin karfe 5:00 na yamma domin ganin likita, inda ma’aikatan asibitin suka sanar da su cewa likitan da aka tsara ba zai samu damar zuwa ba.
Harbo ya ce daga bisani aka sanar da su cewa wani likita mai suna Dr. Ibrahim ne zai maye gurbinsa, yayin da akalla marasa lafiya shida, mafi yawansu tsofaffi masu shekaru sama da 80, ke ci gaba da jiransa.
Ya kara da cewa bayan an tuntubi Dr. Ibrahim ta waya, ya tabbatar zai zo bayan kammala sallar Magariba domin duba marasa lafiyan.
“Da isowarsa, ya fara jin jiri bayan ya fito daga motarsa. Nan take aka garzaya da shi zuwa sashen gaggawa, amma abin takaici, cikin mintuna 15 aka tabbatar da rasuwarsa,” in ji Harbo.
Rasuwar likitan ta girgiza ma’aikatan asibitin da marasa lafiya tare da ‘yan uwansu, musamman ganin cewa ya amsa kiran gaggawa ne domin taimaka wa marasa lafiya da suka dade suna jiran ganin likita. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan musabbabin rasuwarsa ba.
-
News3 days ago
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Basarake Bisa Zargin Kona Wani Mutum Kan Zargin Satar Itacen Girki
-
News2 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Bada Umarnin Binciken Kuɗaɗen Tsaro Na Ƙananan Hukumomi 44 Cikin Mako Biyu
-
News22 hours ago
Shugaban FCAPT: Rajistar Katin Zaɓe Muhimmin Mataki Ne Wajen Ƙarfafa Dimokuraɗiyya
