Connect with us

News

Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Najeriya

Published

on

Trump 768x501

Gwamnatin Amurka ta sanar da janye mafi yawan dakarunta da ta tura Najeriya domin taimakawa a yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.

Sanarwar ta fito ne daga Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Amurka da ke kula da Turai da Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson, yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan Taron Shugabannin Hafsoshin Tsaro na Afirka na shekarar 2026.

A cewarsa, an kammala aikin haɗin gwiwar da aka tura sojojin domin gudanarwa, saboda haka aka janye yawancinsu zuwa Amurka.

Sai dai Janar Anderson ya tabbatar da cewa Amurka ba za ta daina tallafa wa Najeriya ba, domin za ta ci gaba da bayar da gudunmawa ta hanyar musayar bayanan sirri, ba da horo da kuma sauran nau’o’in haɗin gwiwar tsaro.

Ya ce haɗin gwiwar da ke tsakanin Amurka da Najeriya ya taimaka wajen raunana ayyukan ƙungiyar ISIS da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar yankin Tafkin Chadi.

Haka kuma ya yabawa rundunar sojin Najeriya, yana mai cewa tana da ƙwarewa da ƙarfin gudanar da ayyukan tsaro, yayin da haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya samar da gagarumar nasara wajen yaƙi da ta’addanci.

Advertisement

Janar Anderson ya ce haɗin bayanan sirri tsakanin Amurka da Najeriya ya taimaka wajen kai farmakin da ya yi sanadin kashe Abu-Bilal Al-Minuki, wanda ake zargin shi ne mataimaki na biyu a jagorancin ƙungiyar ISIS ta duniya.

Ya kuma yi kira ga ƙasashen Afirka da su ƙara ƙarfafa musayar bayanan sirri domin yaƙar ta’addanci, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da ke ketare iyakokin ƙasashe.

A cewarsa, irin wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen cafke wani jirgin ruwa da ke ɗauke da tan 31 na hodar Iblis a gabar yammacin Afirka, wanda ya bayyana a matsayin mafi girman kama miyagun ƙwayoyi da aka taɓa yi a teku.

An dai tura kusan sojojin Amurka 200 zuwa Najeriya a watan Fabrairun bana domin tallafa wa ayyukan tattara bayanan sirri da yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.

Masana harkokin tsaro na ganin cewa, duk da janyewar yawancin dakarun Amurka, haɗin gwiwar ƙasashen da ke yankin Tafkin Chadi zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen daƙile ayyukan Boko Haram, ISWAP da sauran ƙungiyoyin ta’addanci.

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending