Connect with us

News

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita A Wasu Yankuna Bayan Rikicin Ƙabilanci Da Ya Yi Sanadin Mutuwar Kusan Mutum 80

Published

on

FB IMG 1783421369314

Gwamnatin Jihar Neja ta sanya dokar hana fita a wasu al’ummomin Ƙaramar Hukumar Rafi biyo bayan mummunan rikicin ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin al’ummar Kamuku da Fulani, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 80 tare da jikkata wasu da dama da kuma lalata dukiyoyi.

Gwamnan jihar, Umaru Mohammed Bago, ya sanar da matakin ne yayin ziyarar duba halin da yankunan da rikicin ya shafa suke ciki. Mataimakinsa, Yakubu Garba, ne ya wakilce shi a ziyarar.

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 150, Sun Kwace Babura 100 A Legas

A cewar gwamnan, an ɗauki matakin sanya dokar hana fita ne domin dakile ci gaba da tashin hankalin, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, da kuma bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi.

Ya umarci jami’an tsaro da su tura isassun dakaru da kayan aiki zuwa yankunan da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya da kuma hana rikicin ƙara yaɗuwa zuwa wasu al’ummomi.

Rahotannin binciken farko sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga takaddama kan mallakar filayen noma tsakanin ɓangarorin biyu.

Advertisement

Haka kuma, Gwamna Bago ya umarci Sarkin Kagara, Alhaji Ahmad Garba-Gunna, da ya kafa kwamitin sulhu da sasanci domin shiga tsakani tsakanin al’ummomin da ke rikici, tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai.

Ya kuma yi kira ga al’umma, musamman masu amfani da kafafen sada zumunta, da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da hana sake aukuwar irin wannan tashin hankali.

 

 

 

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending