News
Gwamnatin Kano Ta Kama Gurɓatattun Kayan Abinci Da Abin Sha Na Sama Da Naira Miliyan 300
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kama gurɓatattun kayayyakin abinci da abin sha da darajarsu ta haura naira miliyan 300 cikin ƙasa da watanni huɗu, a wani mataki na kare lafiyar al’umma daga illar kayayyakin da ba su da inganci.
Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano, Dakta Ibrahim Garba Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar domin baje kolin kayayyakin da hukumar ta ƙwace.
Gwamnatin Kano Ta Kama Gurɓatattun Kayan Abinci Da Abin Sha Na Sama Da Naira Miliyan 300
Ya bayyana cewa kayayyakin da aka kama sun haɗa da waɗanda wa’adin amfaninsu ya ƙare, waɗanda aka adana ba bisa ƙa’idojin lafiya ba, da kuma jabun kayayyaki da ke barazana ga lafiyar masu amfani da su.
A cewarsa, hukumar ta ƙara ƙaimi wajen gudanar da sintiri da bincike a kasuwanni da wuraren ajiyar kayayyaki domin gano masu safarar gurɓatattun kaya, tare da tabbatar da an ɗauki matakin doka a kan duk wanda aka samu da hannu.
Dakta Ibrahim ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wani yunkuri na sayar da kayayyakin da ka iya jefa rayuwar jama’a cikin haɗari ba, yana mai gargadin ƴan kasuwa da su guji irin wannan haramtacciyar sana’a.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa tabbatar da inganci tare da duba wa’adin amfani da duk wani kayan abinci ko abin sha kafin su saya, domin kare kansu da iyalansu daga illolin gurɓatattun kayayyaki.
Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da haɗa gwiwa da hukumomin da abin ya shafa wajen tabbatar da cewa kasuwannin Kano sun kasance cike da ingantattun kayayyaki masu aminci ga lafiyar al’umma.
