Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Ƙarin Kuɗin Jarabawar WAEC Da NECO

Published

on

images (11)

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da aka shirya fara aiwatarwa daga shekarar 2027, domin ba da damar ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.

Advertisements
Advertisements

A baya dai, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince da ƙarin kuɗin rajistar jarabawar zuwa Naira 50,000 ga kowane ɗalibi, matakin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki. An bayyana cewa sabon tsarin zai maye gurbin tsoffin kuɗaɗen rajista na WAEC da NECO daga shekarar 2027.

Advertisements

Gwamnatin Legas Ta Kwace Baburan Okada  Sama Da 300

Advertisements
Advertisements

Sai dai, bayan korafe-korafe da suka biyo baya daga ɓangarori daban-daban, gwamnatin ta sanar da dakatar da shirin domin gudanar da ƙarin tattaunawa kafin ɗaukar mataki na ƙarshe. Masana ilimi da dama sun nuna damuwa cewa karin kuɗin na iya hana ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar ci gaba da karatu.

Tun da farko, ƙarin kuɗin jarabawar ya haddasa suka daga wasu manyan ‘yan siyasa da ƙungiyoyi, waɗanda suka bayyana cewa hakan zai ƙara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending