Connect with us

News

Jami’ar Northwest Kano Ta Gabatar da Muhimman Bayanai Kan Lafiyar Al’umma a Tofa

Published

on

images (6)

Jami’ar Northwest Kano ta gabatar da sakamakon binciken lafiyar al’umma (Community Diagnosis) da ɗaliban fannin Likitanci (MBBS) suka gudanar a Unguwar Doka da ke Ƙaramar Hukumar Tofa ta Jihar Kano, domin taimakawa wajen inganta tsare-tsaren kiwon lafiya da ayyukan kula da lafiyar al’umma.

An gabatar da sakamakon binciken ne a wani taro da Sashen Kiwon Lafiyar Al’umma na Tsangayar Kimiyyar Asibiti, ƙarƙashin Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta jami’ar, ya shirya bayan kammala zangon aikin koyon aiki na uku na ɗaliban MBBS.

Da yake jawabi a madadin Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Amina Salihi Bayero, Bursar na jami’ar, Malam Salmanu Muhammad Kibiya, ya ce binciken zai zama muhimmin ginshiƙi wajen tsara manufofi da shirye-shiryen inganta kiwon lafiya a yankin.

Ya ce hulɗa da al’umma na daga cikin manyan manufofin jami’ar, yana mai jaddada cewa Northwest University Kano za ta ci gaba da haɗa koyarwa, bincike da hidimar al’umma domin samar da mafita ga matsalolin da al’umma ke fuskanta.

Ya kuma yabawa al’ummar Unguwar Doka da Hukumar Ƙaramar Hukumar Tofa bisa irin haɗin kai da goyon bayan da suka bayar, wanda ya taimaka wajen nasarar gudanar da binciken.

Tun da farko, Shugaban Taron kuma Provost na Kwalejin Kimiyyar Lafiya, Farfesa Aliyu Abdu, ya yaba wa Hukumar Ƙaramar Hukumar Tofa, sarakunan gargajiya, ma’aikatan lafiya da al’ummar yankin saboda irin gudunmawar da suka bayar.

Advertisement

Ya bayyana cewa an tsara gudanar da binciken ne da farko a Ƙaramar Hukumar Shanono, sai dai matsalolin tsaro suka sa aka sauya wurin zuwa Tofa.

A cewarsa, shirin Community Diagnosis na bai wa ɗaliban likitanci damar gano matsalolin kiwon lafiyar al’umma kai tsaye, tare da ba da shawarwarin hanyoyin magance su bisa hujjojin bincike.

Ya ƙara da cewa tsarin karatun MBBS na jami’ar na da nufin samar da ƙwararrun likitocin da za su iya ba da ingantaccen kulawar lafiya a birane da karkara, tare da fahimtar buƙatun lafiyar al’umma gaba ɗaya.

Rahoton binciken ya mayar da hankali kan lafiyar mata da yara, cututtukan zuciya da jijiyoyin jini, yanayin zamantakewar al’umma da kuma tsaftar muhalli.

Binciken ya shafi mutum 286 daga ƙauyuka uku, inda aka samu cikakken haɗin kai daga hukumomin ƙaramar hukuma, sarakunan gargajiya, ma’aikatan lafiya da mazauna yankin.

Sai dai ɗaliban sun ce sun fuskanci wasu ƙalubale, ciki har da ƙin amsa tambayoyi daga wasu mazauna yankin da kuma yadda gidaje suka kasance ba bisa tsari ba, lamarin da ya kawo cikas wajen tattara bayanai.

Advertisement

Sun ce binciken ya ƙara musu ƙwarewa ta fuskar bincike, sadarwa da kuma amfani da ilimin da suka koya a aji wajen warware matsalolin kiwon lafiyar al’umma.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Tofa, Alhaji Yakubu Ibrahim, ya yabawa jami’ar bisa zaɓar ƙaramar hukumar domin gudanar da binciken, yana mai alƙawarin cewa majalisar za ta yi amfani da sakamakon binciken wajen inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.

Shi ma Dagacin Doka, Alhaji Mustapha Mansur, wanda ya wakilci Hakimin Tofa, ya yaba da wannan yunƙuri tare da buƙatar a ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin jami’ar da al’umma.

Hakazalika, Shugaban Sashen Lafiya na Ƙaramar Hukumar Tofa, Alhaji Sani Abdu, ya yabawa ɗaliban bisa jajircewarsu, tare da ƙarfafa musu gwiwa su bunƙasa rahoton zuwa cikakken kundin bincike da masu tsara manufofin kiwon lafiya za su amfana da shi.

A ƙarshe, Dr. Kabir ya miƙa godiya ga dukkan baƙi da masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar, tare da yabawa mahukuntan Jami’ar Northwest Kano da ɗaliban MBBS bisa nasarar gudanar da wannan muhimmin bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending