Connect with us

News

Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana

Published

on

images (14)

Masana da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun bayyana damuwa kan yadda ake samun ƙarin mata, musamman matan aure, da ke faɗawa cikin ta’ammuli da kuma safarar miyagun ƙwayoyi a wasu sassan ƙasar nan. Sun ce lamarin na zama babbar barazana ga tarbiyyar yara, zaman lafiyar iyali da ci gaban al’umma.

A tsawon shekaru, an fi danganta matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da maza, musamman matasa. Sai dai bayanan baya-bayan nan sun nuna cewa mata ma na ƙara shiga wannan mummunar ɗabi’a, lamarin da ke jawo ƙarin damuwa ga hukumomi da masana.

Jami’an NDLEA Sun Cafke Muggan Kwayoyi Na Sama Da Naira Biliyan 10 Tashar Jiragen Ruwa Ta Apapa

Alƙaluman NDLEA reshen Jihar Kano sun nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yulin shekarar 2026, an kama mutane 904 da ake zargi da hannu a harkar miyagun ƙwayoyi, ciki har da mata 35. Kakakin hukumar a jihar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya ce ko da yake adadin matan bai kai na maza ba, amma abin da ke ƙara tayar da hankali shi ne yadda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da mata, musamman matan aure, wajen adanawa da dillancin ƙwayoyi a cikin al’umma.

A cewarsa, masu wannan haramtacciyar sana’a na yaudarar mata da kuɗi ko wasu alfanun rayuwa, inda wasu ke tsunduma cikin harkar ba tare da mazajensu sun sani ba. Ya kuma bayyana cewa Kano na daga cikin jihohin da matsalar ta fi kamari, inda ake kiyasta cewa miliyoyin mutane na amfani da wasu nau’ikan miyagun ƙwayoyi.

Masana sun yi gargadin cewa idan uwa ta shiga ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi, illar ba ta tsaya gare ta kaɗai ba. Sun ce hakan na iya haifar da tabarbarewar tarbiyyar yara, rushewar zaman iyali da kuma ƙaruwa da matsalolin zamantakewa a cikin al’umma.

Advertisement

Wani bincike da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Dala ta Jihar Kano a shekarar 2025 ya nuna cewa kusan kashi 42 cikin 100 na matan da aka yi bincike a kansu sun taɓa amfani da miyagun ƙwayoyi, musamman magungunan tari masu ɗauke da codeine, tramadol da wiwi. Binciken ya danganta matsalar da talauci, rashin aikin yi, matsin rayuwar aure da kuma ƙarancin ilimi.

Hakazalika, binciken National Drug Use Survey da gwamnatin Nijeriya tare da Hukumar UNODC suka gudanar ya nuna cewa mata na cikin masu amfani da miyagun ƙwayoyi a ƙasar, a cikin kimanin mutane miliyan 14.3 da aka kiyasta suna ta’ammuli da ƙwayoyi.

A lokuta da dama, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga iyaye, shugabannin addini, masu sarautun gargajiya da hukumomi da su haɗa kai wajen dakile matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa ci gabanta tsakanin mata da matasa na iya jefa makomar al’umma cikin haɗari.

A nata ɓangaren, NDLEA ta ce baya ga kama masu hannu a laifuka da dakile safarar miyagun ƙwayoyi, tana ci gaba da wayar da kan al’umma, musamman mata da matasa, kan illolin ta’ammuli da ƙwayoyi domin rage yawaitar matsalar.

Masana sun jaddada cewa shawo kan wannan ƙalubale ba aikin gwamnati kaɗai ba ne. Sun ce dole ne iyaye, malamai, shugabannin addini, ƙungiyoyin al’umma da hukumomin tsaro su haɗa kai domin kare mata da matasa daga fadawa cikin ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi, tare da tabbatar da ingantacciyar makomar iyali da al’umma baki ɗaya..

 

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending