News
An Sace Shugaban Makaranta Da Dalibai Masu Rubuta Jarabawar NECO A Kogi
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wata makarantar sakandare ta gwamnati da ke Odo-Ekina a Jihar Kogi, inda suka sace shugaban makarantar, wani ma’aikacin wucin gadi na Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare (NECO), da wasu ɗalibai yayin da ake rubuta jarabawar NECO.
Jaridar the guardian ta ruwaito ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da ɗalibai ke tsaka da rubuta jarabawa. An ce maharan sun shiga makarantar, lamarin da ya haddasa firgici tsakanin ɗalibai da malamai, kafin su tafi da waɗanda suka sace zuwa wani wuri da ba a sani ba.
An sace Shugaban Makaranta Da Dalibai Masu Rubuta Jarabawar NECO A Kogi
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta sun fara aikin ceto nan take bayan samun rahoton harin. Rundunar ta kuma bayyana cewa an ceto ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutanen.
Har yanzu dai ba a bayyana adadin ɗaliban da aka sace a hukumance ba, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike da kuma farautar waɗanda suka aikata laifin.
