Connect with us

News

Dakarun Sun Dakile Harin ‘Yanta’adda A Iyakar Kano Da Katsina

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun haɗin gwiwa na rundunar sojin Nijeriya da ke Kano, sun yi nasarar daƙile harin ‘yan bindiga tare da hana satar dabbobi a yankin ‘Yankamaye da Rimaye da ke kan iyakar jihohin Kano da Katsina.

Wata sanarwa da Rundunar Sojin Nijeriya ta fitar ranar Alhamis ta bayyana cewa, dakarun sun kama ‘yanta’adda biyu tare da kwato babur daya, da shanu 97, da tumaki 50. Tuni aka mayar da dukkan dabbobin da aka ƙwato ga ainihin masu su, a cewar sanarwar.

An Kama ’Yan Ƙasar Waje Biyu Kan Zargin Shirya Garkuwa Da Mutum A Kwara

Sanarwar, wadda ke ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta Uku ta Sojin Nijeriya, Manjo Babatunde Zubairu, ta ce ‘yanbindigar ɗauke da makamai suna kora dabbobin da suka sata ne a kewayen wuraren Yankamaye da Rimaye.

Ta ƙara da cewa, dakarun sun tare ‘yan bindigar da ke ƙoƙarin tserewa. Sannan bayan musyar wuta ‘yanta’addan sun gudu sakamakon fin ƙarfinsu da dakarun Nijeriya suka yi, lamarin da ya tilasta musu barin dabbobin da suka sace tare da tarwatsewa a gigice zuwa cikin jihar Katsina, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

 

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending