News
Gashash Ya Bukaci Gwamnan Abba Da Gwarzo Su Yi Siyasar Girmamawa Maimakon Cin Mutuncin Juna Don Zaman Lafiya Da Kimar Kano
Fitaccen ɗan kasuwa a Kano kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar A ya buƙaci gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da tsohon mataimakinsa Comrd. Abdussalam Gwarzo su girmama siyasarsu a matsayinsu na manya a jihar Kano maimakon cin mutuncin juna.
Gashash na wannan kiran ne a wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya fitar bayan wasu kalamai da su ka fito daga bakin manyan biyu
Ga wasiƙar
BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KANO, ALHAJI ABBA KABIR YUSUF, DA KUMA TSOHON MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KANO, KUMA ƊAN TAKARAR GWAMNA NA JAM’IYYAR NDC, COMRADE AMINU ABDUSSALAM GWARZO
Roƙo Cikin Girmamawa Domin Zaman Lafiya, Haƙuri da Ɗa’a a Siyasa
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
Ina rubuta wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ne cikin girmamawa, ƙauna da kuma fatan alheri ga ku duka. A matsayina na ɗan Kano, abin da nake buri shi ne ganin jiharmu ta ci gaba cikin zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna.
Da farko, ina yaba wa irin gudummawar da ku duka kuka bayar wajen hidimtawa al’ummar Kano. Tarihi ba zai manta da cewa a wani lokaci kun yi aiki tare domin cigaban wannan jiha ba. Ɗaya ya kasance Gwamna, ɗayan kuma Mataimakin Gwamna. Kun yi aiki kafada da kafada domin cika amanar al’ummar Kano.
Saboda haka, abin takaici ne ganin yadda a yau ake jin kalamai masu zafi da suka na zargi da sukar juna a bainar jama’a tsakanin shugabanni biyu da suka taɓa zama abokan aiki.
Ya Ku Manyanmu,
Siyasa kada ta fi zumunci ƙarfi.
Bambancin ra’ayi a siyasa abu ne na al’ada. Mutane na sauya jam’iyya, yanayi na canzawa, amma wannan bai kamata ya sa mutunci, girmamawa da kyakkyawar alaƙa su gushe ba.
Ku duka manya ne da al’umma ke kallo. Kun haura shekara sittin. Ku iyaye ne, kakanni ne, shugabanni ne, kuma abin koyi ne ga dubban matasa. Maganganunku da ayyukanku suna tasiri sosai. Idan shugabanni suka riƙa musayar zagi da cin mutunci, mabiyansu ma za su kwaikwaya, abin da zai ƙara raba kan al’umma.
Ina roƙonku da ku tuna da tarihin da ya haɗa ku.
Ku tuna lokacin da kuka yi aiki tare.
Ku tuna yadda kuka tattauna matsalolin Kano tare.
Ku tuna yadda kuka yi ƙoƙarin ciyar da jihar gaba tare.
Idan siyasa ta raba ku a yau, kada ta sa ku zama maƙiya. Siyasa tana zuwa tana wucewa, amma mutunci da zumunci su ne abin da ya kamata su dawwama.
Ya Ku Shugabanni,
Dukkanmu ’yan Kano ne.
Dukkanmu ’yan Najeriya ne.
Dukkanmu bayi ne ga ALLAH.
Kuma wata rana duk za mu koma gare Shi.
Babu wanda ya san gobe.
Babu wanda ya san ranar mutuwarsa.
Mulki yana ƙarewa.
Kujera tana ƙarewa.
Jam’iyyun siyasa suna canzawa.
Amma abin da zai rage shi ne kyawawan ayyuka da kyakkyawan suna.
ALLAH Maɗaukakin Sarki Ya ce:
“Kuma ku yi riƙo gaba ɗaya da igiyar ALLAH, kada ku rarrabu.” (Suratul Ali-Imran: 103).
Annabi Muhammad (SAW) ma ya koyar da mu muhimmancin sulhu, yafiya da haɗin kai tsakanin Musulmi.
Wannan wasiƙa ba domin goyon bayan wani bangare ba ce. Roƙo ne ga ku biyun gaba ɗaya.
Hakuri ya fi faɗa daraja.
Sulhu ya fi gaba daraja.
Mutunta juna ya fi cin mutunci amfani.
Al’ummar Kano suna son ganin shugabanninsu suna nuna hikima, dattako da haƙuri, ba saɓani da gaba ba.
Na yi imani iyalanku, abokanku da masoyanku ba sa jin daɗin irin kalaman da ake musayar wa tsakanin ku. Abin da zai fi faranta musu rai shi ne su ga kun sasanta, kun girmama juna, kuma kun zama abin koyi ga matasa.
Jihar Kano tana da manyan ƙalubale da ke buƙatar haɗin kan dukkan shugabanninta, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
Saboda haka, ina roƙonku cikin ladabi:
* Ku bar siyasa ta kasance gasa ta manufofi, ba ta cin mutunci ba.
* Ku fifita zaman lafiya a kan husuma.
* Ku fifita haɗin kai a kan rarrabuwar kai.
* Ku ji tsoron ALLAH a cikin maganganunku da ayyukanku.
* Ku zama abin koyi ga matasa masu tasowa.
A ƙarshe, ina addu’ar ALLAH (SWT) Ya ƙara muku lafiya, hikima da nisan kwana. Ya haɗa zukatan shugabanninmu, Ya ba Kano zaman lafiya da ci gaba, Ya sanya mu cikin waɗanda za su haɗu a kan gaskiya da alheri.
ALLAH Ya shiryar da mu baki ɗaya zuwa ga abin da Yake so kuma Yake yarda da shi. Ameen.
Na Ku Cikin Girmamawa,
Amb. Dr. Mukhtar Gashash
Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano (2027)
Jam’iyyar Accord (AP)
