News
Kotu Ta Bayar Da Belin Shugaban Miyetti Allah Bello Badejo Kan Naira Biliyan 2
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bai wa Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Ƙasa, Bello Bodejo, beli kan kuɗin Naira biliyan biyu (₦2bn) tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa a matsayin masu ɗaukar nauyi.
Mai shari’a Inyang Ekwo, wanda ya yanke hukuncin a ranar Litinin, ya ce dole ne masu tsayawa belin su kasance mutane masu mutunci, inda ɗaya daga cikinsu zai mallaki kadara a yankin Abuja Municipal Area Council (AMAC).
Andy Burnham Zai Karbi Ragamar Mulkin Birtaniya A Matsayin Sabon Firaminista
Kotun ta kuma umurci cewa ɗaya daga cikin masu tsayawa belin ya gabatar da shaidar biyan haraji na shekarun 2023, 2024 da 2025. Haka kuma, Magatakardar Kotun za ta tantance dukkan takardu da bayanan masu belin kafin a cika sharuɗɗan sakin Bodejo.
Baya ga haka, kotun ta umarci Bello Bodejo da ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiya zuwa ƙasashen waje ga kotu, tare da hana shi fita daga Najeriya ko kuma barin yankin ikon kotun ba tare da samun izin kotu ba.
An kuma umarci Magatakardar Kotun ta sanar da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) game da ƙwace fasfon nasa domin tabbatar da bin umarnin kotun.
Daga bisani, Mai Shari’a Ekwo ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranakun 5, 6 da 7 ga Oktoba, 2026.
A ranar 9 ga Yuli, 2026, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da Bodejo a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda 12 da suka shafi zargin halasta kuɗaɗen da ake zargin sun samo asali ne ta haramtacciyar hanya, inda ake zargin lamarin ya shafi kuɗi da yawansu ya kai dala miliyan 2.33.
