News
Kotu Ta Yanke Wa Amarya Hukuncin Kisa Kan Hallaka Mijinta Kwana 9 Bayan Aure A Kano
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wata amarya mai suna Saudat Jibril hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same ta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris, kwanaki tara kacal bayan ɗaura aurensu.
Mai Shari’a Maryam Sabo ce ta yanke hukuncin bayan kotun ta kammala sauraron shaidu da hujjojin da ɓangarorin gwamnati da na wadda ake ƙara suka gabatar.
Yadda Ƙudirin Bunƙasa Noma na Magumeri Ke Maido da Fata ga Manoma
Lamarin ya faru ne a watan Mayun 2025 a unguwar Farawa da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, inda ake zargin Saudat da kashe mijinta bayan sun yi kwanaki tara da aure.
A yayin shari’ar, lauyan gwamnatin Jihar Kano, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya gabatar da shaidu uku domin tabbatar da zargin da ake yi wa Saudat.
Shi kuwa lauyan da ke kare Saudat, Barista Abdulfatah Muhammad, ya gabatar da ita a gaban kotu domin ta kare kanta.
Bayan nazarin hujjoji da shaidun da aka gabatar, Mai Shari’a Maryam Sabo ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin da ake tuhumar Saudat da shi. Saboda haka, kotun ta yi watsi da bayanan kariyar da ta gabatar tare da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Bayan an kammala zaman kotun, jami’an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali suka karɓi Saudat domin ci gaba da aiwatar da matakan da doka ta tanada.
