Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Kama Wanda Ke Kai Wa ’Yan Kayan Aiki A Zamfara

Published

on

WhatsApp Image 2026 08 02 at 11.41.29 (1)

Jami’an tsaro da suka haɗa da rundunar Tsaron Fararen Hula (NSCDC), ’Yan Sandan Nijeriya da Sojoji sun kama wani da ake zargin yana kai wa ’yan bindiga kayan sadarwa da sauran kayayyakin tallafi a Ƙaramar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce an kama wanda ake zargin ne a yankin Bagega yayin da yake safarar kayayyakin da ake kyautata zaton an nufa da su zuwa maboyar ’yan bindiga.

IIIT Ta Horar da Mata ‘Yan Jarida kan Amfani da Kafafen Yaɗa Labarai Wajen Gina Al’umma

Kayayyakin da jami’an tsaron suka ƙwato sun haɗa da na’urorin sadarwa da wasu kayayyakin masarufi da ake zargin za su taimaka wa ’yan bindigar wajen ci gaba da ayyukansu.

Majiyoyin tsaro sun ce wannan nasara ta nuna muhimmancin katse hanyoyin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke samun kayan aiki da sauran tallafin da suke dogaro da shi.

 

Advertisement

 

PRNigeria.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending