Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Musanta Zargi Ware N235.4m Domin Gina Makarantar Da Ba Ta Wanzu Ba A Sumaila

Published

on

img 0773 (1)

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahoton cewa ta ware Naira miliyan 235.4 domin gina ajujuwa a wata makarantar sakandaren ’yan mata da ake zargin ba ta wanzu a Karamar Hukumar Sumaila.

Cibiyar Tracka, wadda ke bibiyar ayyukan gwamnati, ce ta yi ikirarin cewa an ware Naira miliyan 235 da dubu 400 domin gina ajujuwa a GGSSS Massu, da ke yankin Massu a Karamar Hukumar Sumaila.

Gwamnatin Kano Ta Musanta Zargi Ware N235.4m Domin Gina Makarantar Da Ba Ta Wanzu Ba A Sumaila

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce zargin ba shi da tushe, yana mai cewa kudin da Tracka ta ambata ba ya cikin Rahoton Aiwatar da Kasafin Kudin Jihar Kano na Kashi na Hudu na shekarar 2025.

Waiya ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware Naira biliyan 168.35 daga cikin kasafin kudin 2025 mai Naira biliyan 719.557 domin bangaren ilimi, inda aka aiwatar da ayyukan gyaran makarantu, daukar malamai da sauran ayyukan ilimi a fadin kananan hukumomi 44.

Ya bukaci Tracka da ta gabatar da shafin kasafin kudin, lambar NCOA, takardun kwangila, baucan biyan kudi da sunan dan kwangilar da ta dogara da su wajen yin zargin. Ya kuma ce Ma’aikatar Ilimi da SUBEB na gudanar da bincike kan ayyukan ilimi a Sumaila, kuma za a bayyana sakamakon binciken.

Advertisement

Kwamishinan ya jaddada cewa babu wani aiki mai suna “GGSSS Massu, Sumaila – N235.4m” da aka samu cikin kasafin kudin 2025 da aka amince da shi. Ya bukaci jama’a da kungiyoyin farar hula su rika tabbatar da sahihancin bayanan ayyukan gwamnati kafin yada su ga jama’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending