Connect with us

News

Kiwon Lafiya: Kano PHCMB Ta Nemi Ƙarin Haɗin Kan Al’umma

Published

on

IMG 20260818 WA0047

Hukumar Kula da Ayyukan Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta ce za ta ƙara mayar da hankali wajen ƙarfafa hulɗa da al’umma domin ƙara yawan masu amfani da ayyukan kiwon lafiya matakin farko a jihar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin wani taron haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a zauren taron hukumar da ke Kano.

“Mun kama Tsohon Shugaban Karamar  Hukuma  Bisa Zargin Harkar Miyagun Ƙwayoyi ” — Muhuyi Magaji Rimin Gado

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar, inda aka duba yadda ayyukan hulɗa da al’umma suka gudana a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Haka kuma, mahalarta taron sun tattauna kan ci gaban da aka samu wajen ƙara wayar da kan jama’a game da ayyukan kiwon lafiya matakin farko, tare da gano ƙalubalen da ke buƙatar haɗin gwiwar hukumomi da al’umma domin magance su.

Da yake jawabi a wajen taron, Darakta-Janar na hukumar, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya ce haɗin gwiwa da al’umma na da muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin kiwon lafiya matakin farko.

Advertisement

Ya ce al’umma bai kamata su kasance masu karɓar ayyukan kiwon lafiya kawai ba, sai dai su kasance abokan hulɗa wajen gano bukatunsu da kuma taimakawa wajen tsara hanyoyin magance matsalolin da suke fuskanta.

Farfesa Salisu ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su yi amfani da taron wajen duba nasarorin da aka samu, gano gibin da ke akwai da kuma samar da hanyoyin magance ƙalubalen da ke kawo cikas ga samun ayyukan kiwon lafiya.

Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da al’umma da sauran abokan hulɗa domin tabbatar da cewa matsalolin da aka gano sun zama abubuwan da za a ɗauki matakin magancewa a aikace.

A ƙarshe, hukumar ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da sauraron ra’ayoyin al’umma tare da tabbatar da cewa shawarwarin jama’a suna cikin tsarin tsara ayyukan kiwon lafiya da samar da su.

Hukumar ta ce hakan zai taimaka wajen samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya matakin farko wanda ya fi sauraron bukatun al’umma tare da ƙara yawan amfani da ayyukan kiwon lafiya a Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending