Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Tsohuwa Mai Shekaru 101 Da Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Published

on

IMG 20260823 WA0130 750x430

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wata tsohuwa mai shekaru 101, Esther Ogunmabo, bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a garin Ilisan da ke Jihar Ogun.

An kama tsohuwar ne a ranar 15 ga Agusta, 2026, bayan jami’an NDLEA sun cafke ta da gram 90 na skunk, wani nau’in tabar wiwi, wanda ake zargin tana sayarwa ga mazauna yankin cikin ƙananan ledoji.

Donald Duke Ya Sha Alwashin Magance Rashin Tsaro A Arewa Idan Ya Ci Zaben 2027

A cewar hukumar, matar ta shaida wa jami’an cewa ta fara sayar da miyagun ƙwayoyin ne bayan wata gobara ta lalata mata shagon kayan masarufi, lamarin da ya jefa ta cikin matsin rayuwa.

Ta kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin ’ya’yanta da ke zaune a Legas ce ke kawo mata miyagun ƙwayoyin duk bayan kwanaki huɗu, yayin da ita kuma take rarraba su cikin ƙananan ledoji domin sayarwa.

Sai dai, saboda tsufan matar, shugaban NDLEA, Brig. Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayar da umarnin a bayar da belinta tare da sanya ta cikin shirin ba da shawarwari da gyaran hali.

Advertisement

A yayin da aka sassauta wa tsohuwar bisa la’akari da shekarunta, jami’an NDLEA sun kama ’yarta da ake zargi da samar mata da miyagun ƙwayoyin domin ci gaba da bincike kan lamarin.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending