Connect with us

News

Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad

Published

on

1787574944151

Fitacciyar ‘yar siyasa kuma ‘yar gwagwarmaya a Arewacin Najeriya, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta musanta rahotannin da ke cewa ta tura wata tawaga domin ta nemi afuwar Farfesa Isa Ali Pantami kan kalaman da ta yi masa a baya.

Naja’atu ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da tawagar da aka ce ta je wajen Pantami da sunanta, tana mai cewa babu inda ta ba tsohon ministan sadarwa haƙuri.

Singapore Za Ta Tallafawa Yaran Kasar Da Miliyan 90

Ta bayyana hakan ne a wata hira da kafar yaɗa labarai ta BMC, inda ta ce rahoton cewa ta tura mutane domin neman afuwar Pantami ba gaskiya ba ne.

A cewarta, “Pantami da yaransa sun sake fantama min ƙarya, domin babu inda na ba shi haƙuri.”

Naja’atu ta ƙara da cewa ita ba ta zauna da kowa domin shirya irin wannan mataki ba, kuma ba ta ma san da maganar tawagar da ake cewa ta tura ba.

Advertisement

“Ni ban yi zama da kowa ba, ban ma san da maganar ba. Mutane kowa na iya fantama ƙaryarsa,” in ji ta.

Ta kuma jaddada cewa har yanzu tana nan kan matsayinta na baya dangane da kalaman da ta yi game da Pantami, tana mai cewa lamarin da aka ce ta aika tawaga domin neman afuwa bai faru ba.

Rahoton da ake yadawa ya biyo bayan wasu kalamai da Naja’atu ta yi a baya kan Pantami, inda ta yi masa kakkausar suka. A watan Fabrairun 2026 ma, rahotanni sun bayyana cewa ta zargi Pantami da yin kalaman da ta kira ƙarya, tare da yin ikirarin cewa ya taɓa halartar tarukan jam’iyyar ADC.

A wani sabon rahoto da aka wallafa a ranar 23 ga Agusta 2026, an kuma ruwaito cewa Naja’atu ta musanta cewa ta tura tawaga ta musamman domin ba Pantami haƙuri, tana mai cewa babu wanda ta aika domin neman afuwar sa..

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending