News
Dino Melaye Ya Yi Barazanar Maka Shugaban Hukumar Haraji Ta Kasa A kotu
Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce zai garzaya kotu domin kalubalantar nadin Shugaban Hukumar Harajin Najeriya (NRS), Zacch Adedeji, a matsayin Mataimakin Daraktan Tara Kuɗaɗen Kamfen na Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Melaye, wanda yana cikin jiga-jigan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Kogi, ya ce nadin Adedeji na iya haifar da rikicin muradun aiki, kasancewar sa ma’aikacin gwamnati ne da kuma an ba shi wani muƙami a kwamitin kamfen na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jami’an ’Yan Sanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Makarfi
A cewar Melaye, zai nemi kotu ta fayyace ko nadin Adedeji ya yi daidai da dokokin aikin gwamnati da kuma ƙa’idojin da’a da suka shafi ma’aikatan gwamnati.
Tsohon Sanatan ya kuma soki matakin da Shugaba Tinubu ya ɗauka na jagorantar kwamitin kamfen ɗinsa da kansa, yana mai cewa hakan na iya zama alamar rashin cikakken amincewa da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC.
A jerin sunayen kwamitin kamfen da APC ta fitar, an bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin Shugaban Kwamitin Kamfen, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, suka kasance Mataimakan Shugaban Kwamitin.
An kuma naɗa tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zama Sakataren Kwamitin.
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, shi ne Daraktan Tara Kuɗaɗen Kamfen, yayin da Zacch Adedeji aka naɗa a matsayin mataimakinsa.
Melaye ya ce matakin kai ƙarar zai mayar da hankali ne kan tantance sahihancin nadin Adedeji da kuma ko kasancewarsa ma’aikacin gwamnati ya ba shi damar riƙe irin wannan matsayi a kwamitin kamfen na siyasa.
