Connect with us

News

Ƴan kasuwar rodi sun yi zanga-zangar lumana a Kano

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Ƴan rodi da ke kasuwar Kofar Ruwa a Jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa da matakin Ƙaramar Hukumar Dala na yanka sabbin shaguna a cikin kasuwar.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa ƴan kasuwar sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne a cikin kasuwar a jiya Juma’a da safe bisa jagorancin shugaban kasuwar, Alhaji Isyaku Salisu.

Da ya ke zantawa da manema labarai, shugaban kasuwar ya ce sun gudanar da zanga-zangar ne domin bayyana damuwarsu ga sabbin shagunan da a ke shirin samarwa a kasuwar.

Advertisement

A cewar sa, yin hakan ya saɓawa doka, sabo da yanzu haka suna gaban kotu a kan lamarin, inda ya nuna ɓacin amma duk da haka shugabancin Ƙaramar Hukumar ya aiko a na washe musu kayan sana’arsu don yin shagunan.

” Kawai mun wayi gari wasu sun zo wai su na kokarin kwashe mana kaya. Amma dai ba zamu hana su ba kawai mun nemi su nuna mana shaidar daga Inda su ke, sannan kuma mu ƙirga kayan mu saboda halin yau”. Inji shugaban kasuwar.

Salisu ya kuma yi kira ga gwamanan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ya duba halin kunci da ƴan kasuwar rodin za su shiga idan a ka yi shaguna, a don haka ya buƙaci gwamnan da ya sanya baki kan lamarin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending