News
Shugaba Tinubu Ya Nemi Kotun Amurka Ta Hana FBI Da DEA Fitar Da Bayanansa
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shigar da ƙara a wata kotun tarayya a Amurka domin ƙalubalantar sakin wasu bayanan binciken hukumomin Amurka da suka shafi wani tsohon bincike da ya shafi shi.
Lauyoyin Tinubu sun roƙi kotun da ta hana ko ta takaita sakin bayanan da FBI da DEA suka tattara, suna masu cewa fitar da bayanan na iya tauye haƙƙinsa na sirri.
Rikicin Kan N200 Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 3 Da Ƙone-ƙone A Legas
Batun ya samo asali ne daga ƙarar Aaron Greenspan, wani mai fafutukar neman a fitar da bayanan gwamnati, wanda ya nemi hukumomin Amurka su saki takardun da suka shafi binciken da aka gudanar kan Tinubu a farkon shekarun 1990.
Daga cikin bayanan da Greenspan ke nema akwai fayilolin FBI da kuma bayanan tambayoyin jami’an hukumar da aka gudanar tsakanin 1992 zuwa 1993.
Haka kuma, ƙarar ta shafi wasu bayanai da suka danganci wata shari’ar kwace kuɗi ta shekarar 1993 da ta shafi kusan dala 460,000.
Tinubu ya musanta aikata wani laifi.
Lauyoyinsa sun ce kasancewar wasu bayanai sun taɓa bayyana a bainar jama’a ba yana nufin cewa a saki dukkan bayanan binciken ba.
Sun roƙi kotun da ta amince da ci gaba da ɓoye ko goge wasu sassa na bayanan bisa dalilan kare sirri da tanadin dokokin Freedom of Information Act.
Greenspan dai ya shigar da ƙarar neman bayanan ne ƙarƙashin dokar Freedom of Information Act (FOIA), kuma shari’ar tana gudana a Kotun Gundumar Amurka ta District of Columbia.
A yanzu, kotun ce za ta yanke hukunci kan ko hukumomin Amurka za su saki bayanan da ake nema gaba ɗaya, ko kuma su ci gaba da ɓoye ko rage wasu daga cikinsu.
-
News2 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News5 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News3 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
