News
An Cafke Wata Mahaifiya Bisa Zargin Kai Wa Ɗanta Miyagun Ƙwayoyi A Gidan Yari
Jami’an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wata mata, Mrs Iyabo Sowunmi, bisa zargin ƙoƙarin shigar da ƙwayar da ake zargin haramtacciyar ƙwaya ce cikin gidan gyaran hali da ke Ibara, Abeokuta, Jihar Ogun.
Ana zargin matar da ƙoƙarin kai wa ɗanta, Dare Sowunmi, ƙwayar, wanda ke tsare a cibiyar bayan da wata kotu ta yanke masa hukuncin kisa.
Kamfanin OPay Ya Karyata Jita-jitar Dakatar Da Ayyukansa
Kakakin hukumar a Jihar Ogun, Olayinka Odukoya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Ya ce an kama Sowunmi ne da misalin ƙarfe 1:33 na rana ranar Juma’a, 28 ga Agusta, 2026, yayin da jami’an tsaro ke gudanar da binciken ababen da ake shigar da su cikin cibiyar.
A cewar Odukoya, jami’an sun gano wani abu da ake zargin ƙwayar “Colos” ce, wadda ke da tasiri ga kwakwalwa, a ɓoye cikin wata ƙaramar leda ta garin abin sha.
Ya ce ana zargin an shirya kai ƙwayar ne ga wani fursuna da ke tsare a cibiyar.
“Bayan gano abin, jami’an tsaro sun gaggauta tsare Mrs Sowunmi. Daga bisani, bisa tsarin haɗin gwiwar hukumomin tsaro, an miƙa ta ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu,” in ji shi.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwantrolan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Jihar Ogun, Abioye Adesina, ya yaba wa jami’an tsaron bisa taka-tsantsan da suka nuna.
Adesina ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin tsaro domin hana shigar da abubuwan da ba a yarda da su ba cikin gidajen gyaran hali.
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News5 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News2 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
