Connect with us

News

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci Da Rashawa Na Jihar Kano Ya Yi Murabus

Published

on

IMG 20260916 WA0030

Shugaban Hukumar Korafe-Korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Sa’idu Yahaya, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Wata majiya ta ruwaito cewa Sa’idu ya yi murabus ne sakamakon matsin lambar da ake zargin gwamnatin jihar ta yi masa kan yadda yake gudanar da hukumar.

Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye Da 1000 A Shekara Ɗaya

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Sa’idu Yahaya da gwamnatin Jihar Kano ba su tabbatar da labarin murabus ɗin a hukumance ba.

An naɗa Sa’idu Yahaya a matsayin shugaban PCACC a watan Agustan 2025, bayan kammala wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da naɗinsa, inda aka ba shi wa’adin shekaru biyar na jagorantar hukumar.

Advertisement

A watannin baya-bayan nan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi suka kan yadda ake tafiyar da hukumar, inda ya bayyana rashin gamsuwarsa kan ayyukan da hukumar ke gudanarwa.

Wata majiya ta ce matsin lambar da aka samu kan shugaban hukumar na da alaƙa da damuwar da ake da ita kan yadda hukumar ke gudanar da aikinta da kuma abubuwan da ake sa ran za ta cimma.

Sa’idu Yahaya ya kasance ma’aikacin wata hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta gwamnatin tarayya kafin naɗinsa a matsayin shugaban PCACC na Kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending