News
Maniyyatan aikin Umrah sun zargi Azman Air da zubar da su a Kano
Daga kabiru basiru fulatan
Wasu maniyyata aikin Umrah sun zargi kamfanin sufurin jiragen sama na Azman Air da zubar da su a Kano, suna watangarari bayan ya gaza kai su ƙasa mai tsarki.
Maniyyatan waɗanda suka ce sun kai ɗaruruwa, sun koka kan rashin ba su ko da makwanci bayan sun baro gidajensu daga jihohi daban-daban.
Wasu maniyyatan sun shaida wa BBC cewa, sun shiga mawuyacin hali bayan Azman Air din ya zubar da su a Kano ba tare da yi musu bayani a kan tsaikon da aka samu na jigilarsu zuwa kasa mai tsarki ba.
Daya daga cikin fasinjojin, ya shaida wa BBC cewa, kusan kwanansu biyu sun jibge a Kano, kuma akwai wadanda daga cikinsu suka je Kanon daga jihohi kamar Sokoto da Kebbi da Zamfara da Borno har ma Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Fasinjan ya ce an bar su zube ba tare da an basu makwanci ba.
Ya ce “Da muka je Kano cikin dare mun zauna filin jirgin saman Kano har zuwa 11:30 na dare, ba wanda ya ce mana uffan, haka muka yi ta zaman jira har muka gaji, daga nan ne mu shiga gari muka nemo otel don mu kwanta.”
‘Babu sisin wani maniyyaci a hannunmu’
Saudiyya ta ce mutum miliyan daya za su yi aikin Hajjin bana
Asarar da Saudiyya ke yi saboda rashin mahajjata daga kasashen duniya
Fasinjan ya ce, sun je ofishin Azman Air din dake Zaria Road, sun tarar an kulle, haka suka kasance ba bu wnada ya ce musu komai har sun gaji da biyan kudin otel.
Mutumin ya ce,”Ni har aikin Umrah ma ya fitar mini a rai, gara a mayar mini da kudina na koma gida.”
Shima wani fasinjan ya shaida wa BBC cewa, suna da yawa wadanda aka watsar da su ba tare da yi musu bayanin komai ba, don sun kai kusan mutum 500, in ji shi.
To sai dai mataimakin babban manajan kamfanin na Azman Air, Nuradden Aliyu, ya shaida wa BBC cewa, jinkirin da aka samu ya samu asaline sanadin fashewar tayar jirginsu a makon daya wuce a kasa mai tsarki lamarin da ya haddasa tashin wuta amma an yi nasarar kasheta.
Ya ce wannan hatsari ne ya shafi lafiyar jirginsu na jigilar aikin Umrah kodayake tuni aka kammala gyaransa a ranar Litinin 18 ga watan Aprilun, 2022.
Mataimakin babban manajan kamfanin na Azman Air, ya ce ana sa ran tasowar jirgin zuwa Najeriya don ci gaba da aikin jigilar a ranar Talata 19 ga watan Aprilun, 2022.
Ya ce sai da suka tuntubi wasu kamfanonin jiragen amma saboda yanayin da ake ciki na jigilar zuwa Umrah, basu samu jirgin da zai taimaka musu ba, shi ya sa suka tsaya tsayin daka wajen ganin an gyara na su.
Nuradden Aliyu, ya ce,” Duk wani matsayi da muke ciki mu kan sanar da fasinjoji cewa mun daga jirginsu kada suje filin jirgin sama.”
Ya ce, an samu rashin fahimta tsakaninsu da maniyyatan, saboda shi aikin Umrah, kamfanonin da ke shirya tafiye-tafiye ne ke siyan tikitin tafiya, su kuma a na su bangaren sun sanar da duk wadanda suka kamata.
Fasinjojin da BBC ta tattaunawa da su, sun bukaci kamfanin Azman Air da ya biyasu kudaden da suka kashe kamar na wajen kwana da suka kama a Kano tare da sauran wahalhalun da ya janyo musu.
To amma kamfanin ya ce ba bu wani hakkin fasinja da zai salwanta a hannunsa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
