Connect with us

News

Shugaban Kwalejin Sa’adatu Rimi Ya Taya Sabon Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi Farfesa Sani Lawan Malumfashi Murna

Published

on

IMG 20261103 150708 075
Shugaban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Dakta Kabiru Ahmad Gwarzo,
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Shugaban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Dakta Kabiru Ahmad Gwarzo, ya taya Farfesa Sani Lawan Malumfashi murnar naɗa shi Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Jihar Kano.

Dakta Gwarzo ya bayyana naɗin Farfesa Malumfashi da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi a matsayin matakin da ya dace, yana mai cewa an sanya ƙwarya a gurbin kwarya.

Wasu Ƴan bindiga Su Yi Garkuwa Da Makafi Biyu A Filato

A cikin saƙon taya murnar da ya aikewa manema labarai, shugaban kwalejin ya bayyana fatansa na ganin sabon kwamishinan ya samu nasara wajen gudanar da ayyukansa, musamman waɗanda suka shafi bunƙasa harkokin ilimi a jihar.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba Farfesa Malumfashi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa, tare da samun nasarar aiwatar da shirye-shiryen ci gaban ilimi.

Dakta Gwarzo ya ce naɗin zai taimaka wajen ƙarfafa manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na bunƙasa harkokin ilimi a Kano.

Advertisement

Ya kuma tabbatar da cewa Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi a shirye take ta bayar da gudunmawar da ta dace wajen tallafa wa sabon kwamishinan domin cimma manufofin inganta ilimi mai zurfi a jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending