News
Yan Bindiga Sun Sace Daliban Islamiyya 14 Da malamansu A Neja
Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban makarantar Islamiyya 14 tare da malaminsu a ƙauyen Tungan-Bako da ke gundumar Pandogari, ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.
An sace mutanen ne a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, lokacin da suke girbin masara a gonar malaminsu.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce ɗaliban na taimaka wa malaminsu ne wajen girbin masarar kafin maharan su afka musu.
Ya ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun fara aikin ceto domin kuɓutar da waɗanda aka sace.
Rahotanni sun nuna cewa kafin sace su, ɗaliban sun tsaya a wani rijiya domin wanke jikinsu da shan ruwa a lokacin da suke komawa gida, inda maharan suka yi awon gaba da su.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankunan karkara na jihar Neja, musamman kan manoma da al’ummomin da ke zaune a ƙauyuka.
A baya-bayan nan, an samu sace manoma 47 a ƙaramar hukumar Mariga a watan Satumba, yayin da a watan Agusta aka ruwaito sace masu ibada sama da 500 a wasu masallatai a jihar.
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News20 hours ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Tsawaita Dakatarwar Da Ta Yi Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomin Rogo, Bagwai Da Bebeji

