Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun  Bankado Gidan Da Ake Noma Tabar Wiwi A legas

Published

on

IMG 20261103 170006 447
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta gano wani gida da ake zargin ana amfani da shi wajen noman tabar wiwi a cikin gida a yankin Apapa, tare da kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

Waɗanda aka kama sun haɗa da wani ɗan ƙasar Poland, Thomas Razvickas, mai shekaru 49, da wani ɗan Najeriya, James Chisome, mai shekaru 36.

Jami’an Ƴansanda Sun Bankado Wurin Buga Jabun Kudi Na Dalar Amurka A Ondo

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abimbola Adebisi, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce an kama mutanen ne da misalin ƙarfe 8:15 na safiyar ranar 2 ga Nuwamba, 2026, bayan samun bayanan sirri.

A cewarta, binciken gidan ya gano wasu na’urori da kayan aikin da ake amfani da su wajen shuka, girbe da sarrafa tabar wiwi.

Ta ce mutanen biyu, waɗanda ke zaune a gidan, sun riga sun bayar da bayanansu ga masu bincike, kuma suna taimaka wa jami’an tsaro wajen gudanar da binciken da ake yi.

Advertisement

Sai dai rundunar ba ta bayyana adadin tabar wiwi da aka samu a gidan ba, ko yawan wadda aka girbe, da kuma tsawon lokacin da ake gudanar da aikin a wurin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da hukumomin yaƙi da miyagun ƙwayoyi suka gano wuraren sarrafa ƙwayoyi a cikin gidajen zama a Legas ba.

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending