News
Duk da Ganduje ya nuna Gawuna a matsayin ɗan takara, sai na kara da shi a zaɓen fidda-gwani — Inuwa Waya
Daga khadija Abdullahi muhmd
Na gaba-gaba a ƴan takarar gwamnan Kano a jam’iyar APC, Inuwa Waya, ya ci alwashin sai ya shiga zaɓen fidda-gwani da Mataimakin Gwamnan jihar, Nasiru Gawuna, wanda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya zaɓa a matsayin ɗan takara a zaɓen 2023.
A ranar Asabar da daddare ne dai Ganduje ya zaɓi Gawuna a matsayin wanda zai tsaya takarar gwamnan Kano na zaɓen 2023, inda Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo, zai zame wa Gawuna mataimaki.
Sai dai kuma Waya ya ƙi amince wa da wannan mataki na gwamnan, inda ya baiyana cewa a yau Litinin na zai je ya siyo fom ɗin shi na takara, kamar yadda ya shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN.
“A naɗa ka ɗan takara wani abu ne daban, kuma wani abu ne daban ka fito a matsayin ɗan takara. Ni har yanzu Ban janye takara ta ba. Kuma wannan mataki da gwamnan ya ɗauka ba zai kawo cikawa a kuduri na na samar da mulki mai inganci a Kano ba.
“Muna da yakinin APC za ta baiwa ko wanne ɗan takara dama ya fafata a zaɓen fidda-gwani, kuma ina da ƙwarin gwiwa cews ni zan lashe zaɓen na fidda-gwani da ma babban zaɓen.
“A gobe (yau Litinin) zan je in sayi fom ɗin takara kuma ina kira ga magoya baya na da su kwantar da hankalin su, sannan su ci gaba da ba mu goyon baya har mu samu tikitin takarar gwamna a APC,” in ji shi.
Waya ya kuma musanta cewa Ganduje ya titsiye shi a kan wai ya bashi maƙudan kuɗaɗe domin ya tsayar da shi a matsayin ɗan takara, inda ya ce “wannan labarin ƙarya ne kuma yarfe ne.
“Babu wani lokaci da Ganduje ya titsiye ni wai a kan na bashi kuɗi ya tsayar da ni takara. Sannan babu wani lokaci da na baiwa Gwamna kuɗi domin ya tsayar da ni takara. Wannan sharri ne,” in ji Waya.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
