News
Amurka ta ƙaryata cewa ɗakunan binckenta ke baza ƙyandar biri daga Najeriya
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da wata sanarwa da ke Allah-wadai da abin da Amurka ta bayyana “labarin ƙarya da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta” da ke alakanta ɓarkewar cutar ƙyandar biri a duniya “daga dakunan bincikenta a Najeriya”.
Jarumin Fina-Finan Nollywood, Jim Iyke, Ya Musulunta
Sanarwar ta ce irin waɗannan rahotannin “karairayi ne tsantsa” tana mai cewa babu wasu daƙunan binciken lafiya na Amurka a Najeriya.
A ranar 27 ga watan Mayu, ƙasar Rasha ta buƙaci hukumar lafiya ta duniya (WHO) da ta yi binciken ɗakunan bincken lafiya a Najeriya na Amurka a Abuja da Zaria da Lagos da ke da nasaba da yaduwar cutar kyandar biri a duniya.
A 1970 aka fara samun ɓullar ƙyandar biri a Afirka kuma tun lokacin ake samun rahotannin cutar a wasu yankuna na nahiyar.
A baya-bayan nan cutar ta ɓulla a ƙasashen Turai da arewacin Amurka da sauransu.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
