News
MA SU RUWA DA TSAKI NA APC SUN MAGANTU KAN TIKITIN MUSULMI DA MUSULMI
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Kungiyar masu ruwa tsakin jam’iyyar APC ta ce kada jam’iyyar ta yi kuskuren yin tikitin Musulmi da Musulmi a kasar nan
Shugaban Kungiyar, Aliyu Audu, ya sanar da cewa yin hakan zai matukar raba kan talakawa kuma zai tabbatar da rashin zaman lafiya
Ya kara da bayyana cewa, jam’iyyar kada ta yi kuskuren, domin shugaba nagari zai iya zama Musulmi ko Kirista
Masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC sun yi kira ga shugabancin jam’iyyar da Kungiyar Progressive Governors da su tsaya neman mataimakin ‘dan takarar shugabancin kasa kan Kiristocin arewa.
Punch ta ruwaito cewa, damuwarsu tana da tushe ne bayan cece-kuce ya yi yawa kan tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya janyo maganganu daban-daban a kwanakin da suka gabata.
A yayin jawabi a wani shiri na shagalin bikin ranar damokaradiyya, Shugaban Kungiyar masu ruwa da tsakin APC na kasa, Aliyu Audu, ya bayyana bukatar watsi da duk wani abu da zai sa a dauko mataimaki Musulmi domin tabbatar da cigaban hadin kan kasar nan.
Ya ce, “Dalilin da yasa muka ankare da cewa kada addini ya zama madogara wurin zaben shugaba. Halin da kasar nan ta tsinci kanta a ciki yasa muka yanke wannan shawarar, matukar sun damu da rayukanmu.
“A yau, kasar mu ta rabe a bangaren kabilanci da addini kuma ba za mu iya zuba ido a wannan abu mai muhimmanci ba.
“Wannan ne dalilin da yasa muke tunanin dole a saka APC a hanya yayin zaben mataimakin ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Audu ya ce, kin bin wannan shawarar zai assasa wutar rabuwar kan talakawa kuma ya kawo rabewar kai.
Kamar yadda yace, Najeriya tana bukatar shugabanci nagari, wanda zai iya zuwa daga shugaba Musulmi ko Kirista.
Ayokunle wanda ya samu wakilcin Wale-Oke, shugaban Pentecostal Fellowship of Nigeria, ya ce duk jam’iyyar da ke son samar da shugaban kasa na gaba dole ne ta hada kai da yankunan Kiristoci.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
