News
Kotu ta yanke wa Mama Boko Haram shekaru biyar a gidan yari
Daga mujahid danlami garba
Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati a Najeriya EFCC ta sanar da samun nasara a kotu, bayan da aka yanke wa Aisha Wakil, da aka fi sani da Mama Boko Haram, da wasu mutum biyu daurin shekara biyar a gidan yari.
An nada sabon Sarkin Kwatarkwashi
Mai sharia Aisha Kumaliya ta babbar kotun jiha a Maiduguri ta kama Aisha Wakil, da Tahiru Sai’du da kuma Prince Lawal Shoyode da laifin almundahanar naira miliyan 71,400,000.
Daurin kuma zai kasance ba tare da damar biyan tara ba a cewar mai shariar.
Tun a watan Satumban 2020 ne aka sake gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu bisa zarge-zarge biyu, na almundahanar ta sama da naira miliyan 71.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
