Connect with us

News

Majalisar dokokin Kano ta bada umarnin dakatar da gina shaguna da akeyi a kofar shiga asibitin “IDH” da ake kira asibitin (Zana).

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

Majalisar dokokin Kano ta bada umarnin dakatar da gina shaguna da akeyi a kofar shiga asibitin “IDH” da ake kira asibitin (Zana).

Advertisement

 

Majalisar ta bayar da umarnin ne a zamanta na Larabar nan.

Yadda ɗaruruwan mutane ke rububin ɗiban ruwa a wata ƙatuwar rijiya a Indiya

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Fagge, Tukur Muhammad Fagge, ne ya gabatar da kudirin gaggawa inda kuma ya samu amincewar majalisar.

 

Tukur Muhammad Fagge, ya ce gina shaguna a kofar asibitin zai kawo barazana ga marasa lafiya dake zuwa asibitin.

Advertisement

 

Majalisar ta kuma kafa kwamitin bincike kan batun gina shagunan karkashin kwamitin lafiya da kasa da kuma Muhalli na majalisar inda ta umarci kwamitin da ya gabatar da rahotansa a ranar Talata mai zuwa 21 ga watan da muke ciki.

 

Wakilin mu na majalisa Aminu Abdullahi Ibrahim ya ruwaito cewa majalisar ta dage zamanta zuwa ranar Litinin 20 ga watan Yunin da muke ciki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending