Connect with us

News

An Kama Shi Kan Azabtar Da ’Yar Aiki Da Wuta Kan Keken ’Ya’yansa

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

Wani magidanci ya shiga hannu kan yi wa ’yar aikinsa azaba da karfen da aka sanya a wuta bisa zargin hawa keken ’ya’yansa.

Advertisement

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Imo ta cafke magidancin ne bayan ya sanya karfe a wuta, ya rika yi wa yarinyar mai shekara 12 lalas da shi a mazaunanta.

Birtaniya ta kulla yarjejeniya da Najeriya kan korar bakin-haure

Advertisement

 

An tsare mutumin ne da taimakon wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Darlington Chidera Ibekwe, bayan bidiyon aika-aikan da mutumin ya aikata ya karade kafofin sada zumunta na zamani.

Advertisement

Kakakin ’yan sandan jihar, Mike Abattam, ya shaida wa wakilinmu cewa magidancin na tsare a Ofishin ’Yan Sanda na New Owerri, muka za a mika shi domin amsa tambayoyi a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar.

Jami’in ya ce an kai karamar yarinyar asibiti domin ba ta kula wa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending