Business
Shafin Twitter ya maka gwamnatin Indiya a gaban kotu
Daga yasir sani Abdullah
Shafin Twitter, ya maka gwamnatin Indiya a gaban kotu bayan da aka ba shi umarnin cire wasu abubuwa da aka wallafa a dandalinsa.
Twitter ya bayyana bukatun gwamnatin kasar mai bin addinin Hindu a matsayin ko dai na son zuciya ko kuma rashin daidaito.
Gwamnatin Indiya ta ce dole ne duk kamfanonin sadarwar sada zumunta su bi dokokin cikin gida.
Dokar kamfanin fasahar dai ta ba wa kamfanin damar cire duk wasu bayanai da aka wallafa da ka iya haiar da barazana ga harkokin tsaron kasa.
Sai dai kuma masu fafutuka na sukar gwamnati kan toshe shafukan masu sukar ta.
Kamfanin dai na da kimanin masu amfani da shi miliyan ashirin da hudu a Indiya.
Advertisements
