Connect with us

News

Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza, -Ndume.

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

Advertisement

 

Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin soji, Ali Ndume, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar kan tabarbarewar tsaro a kasar.

Advertisement

GIDAN YARIN KUJE: GWAMNATI TA FITAR DA SUNAYEN MUTANEN DA SUKA TSERE

Rahoton Premium Times Mista Ndume, dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai wakiltar Borno ta Kudu, dangane da mummunan harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, ya ce shugabancin kasar ya gaza a babban kudirin sa na ga ‘yan kasa.

Advertisement

Mista Ndume, a ranar Alhamis a wata hira da yayi a gidan talabijin na Channels, ya ce da harin ba zai yiwa yanta’adan sauki ba inda gidan yarin ya kasance da isassun makamai da isassun ma’aikata. “Na tabbata da jam’ian tsaro sun gaggauta kai dauki da an samu nasarar dakile harin amma sun dauki tsawon sa’o’i hudu a gidan yaro babu taimako daga koina,” in ji Sanatan.

Senata Ndume ya koka da yadda gwamnati mai ci a yanzu ke sanya mutanen da ba su iya aiki ba shugabanci a wurare masu muhimanci.

Advertisement

Da yake nuna goyon bayan ga ‘yan Najeriya , Sanatan ya nuna rashin jin dadinsa da yadda masu magana da yawun shugaba Buhari ke fitar da jawabi iri daya a duk lokacin da irin wannan bala’i ya faru. Ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya kasance mai yiwa al’ummar kasa bayani a irin wadannan lokuta, ba masu taimaka masa kan harkokin yada labarai ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending